Mar 14, 2018 06:23 UTC
  • Bakin Haure 'Yan Afrika Fiye Da 16,000 Ne Aka Mayar Da Su Kasashensu Daga Kasar Libiya

Babbar jami'a mai kula da siyasar harkokin wajen kungiyar tarayyar Turai ta bada labarin cewa: Bakin haure 'yan kasashen Afrika fiye da 16,000 ne aka koma da su kasashensu daga kasar Libiya.

Babbar jami'a mai kula da siyasar harkokin wajen kungiyar tarayyar Turai Federica Mogherini ta sanar da cewa: Bakin haure fiye da 16,000 ne da suka fito daga kasashen Afrika da suke rayuwa a sansanonin 'yan gudun hijirar Libiya aka koma da su kasashensu daga farkon watan Janairu zuwa watan Fabrairun wannan shekara.

Dangane da batun cewa ana sayar da bakin haure a matsayin bayi a kasar Libiya: Mogherini ta bayyana cewa daukan matakin mayar da bakin hauren zuwa kasashensu zai warware wannan matsala, kuma babban aikin da kungiyar tarayyar turai da sanya a gaba ke nan, don haka bakin ahuren da suka rage a sansanin 'yan gudun hijirar kasar ta Libiya a halin yanzu basu shige mutane 4000 zuwa 5000 ba.    

Tags