Jun 12, 2018 12:12 UTC
  • Kwamitin Tsaron MDD Ya Kara Wa'adin Takunkumin Da Ya Kakaba Kan Kasar Libiya

Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya ya kara wa'adin takunkumin da ya kakaba kan kasar Libiya na tsawon shekara guda.

Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya a yayin zamansa a jiya Litinin ya amince da daftarin kuduri mai lamba 2420 da kasar Birtaniya ta gabatar kan neman karin wa'adin takunkumin da kwamitin tsaron ya kakaba kan kasar Libiya na tsawon shekara guda cur.

Dukkanin mambobin kwamitin tsaron 15 ne suka kada kuri'ar amincewa da kudurin wadda tun a watan Yunin shekarar da ta gabata ta 2017 ce kwamitin ya kada kuri'ar amincewa da kuduri mai lamba 2357 kan kakaba takunkumi kan kasar ta Libiya na tsawon watanni 12, kuma takunkumin ya hada da haramta sayarwa kasar makamai.  

Tags